Da gaske ne Buhari ya kori gwamnan CBN?

A farkon makon nan ne shafin Facebook na Hope For Nigeria ya ruwaito wani labari da ke cewa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kori Gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele daga aikinsa.
Shugaba Buhari ya kori Mista Emefiele kuma ya zabi sunayen mutum biyu daga yankin arewacin kasar don zabar wanda zai maye gurbinsa daga cikinsu, kamar yadda labarin ya yi ikirari.
Labarin wanda aka yada sau fiye da 2,500, ya ce "Shugaba Buhari ya umarci Gwamnan CBN Godwin Emefile da ya tafi hutun aiki ne" domin maye gurbinsa da wani.

Wani tsohon daraktan sadarwa ga tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, Jackson Ude, shi ma ya wallafa labarin a Twitter, inda aka yada shi sau sama da 500.
Mene ne gaskiyar labarin?
Dokar da ta kafa bankin CBN ta shekarar 2007 ta tanadi cewa shugaban kasa ba shi da ikon cire gwamnan CBN har sai ya samu sahalewar biyu cikin uku na mafi yawan 'yan majalisar dattawa.
Wa'adin Gwamnan CBN na shekara biyar zai kare ne ranar 3 ga watan Yunin shekarar 2019.
Mai magana da yawun CBN Isaac Okorafor ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa labarin "kanzon-kurege ne", inda wani ma'aikacin bankin kuma ya ce "gwamnan yana ofis a ranar Litinin kuma ranar Talata ma ya gana da manoman auduga."
Garba Shehu mai magana da yawun fadar shugaban kasar Najeriya ya ce babu gaskiya a labarin, saboda haka "na boge ne".

Post a Comment

0 Comments