Matsaloli 6 da zasu sa karasa aikin NPOWER yayin cikawa

Wasu matsaloli guda shida (6) da idan sun faru a lokacin cike N-POWER tana iya sa mutum yayi rashin shiga cikin shirin.
1. Na farko kada a samu bam-bancin sunan ka dake kan BVN da sunan dake kan account dinka na banki, misali:
Sunan dake kan account dinka Musa Idris, akan BVN dinka kuma Idris Musa, akwai matsala a nan.
Dole sai ya zama abinda yake kan BVN ya dace da wanda yake kan account name.
Amma wannan da sauki akan na biyu dake tafe 👇
.
2. Misali sunan ka dake kan BVN AbdulMuminu Sani, wanda yake kan account kuma AbdulMumin Sani.
Idan ka lura a na farko akwai (U) na biyu kuma babu (U) AbdulMumin da AbdulMuminu.
Idan mutum cika N-POWER da wannan bam-bancin da wahala ya samu.
Saboda sun sha wahalan haka da mutane a farkon N-POWER 2016, daga lokacin suka ce ba zasu sake yarda ba.
-
Sannan ka tabbatar date of birth dinka da yake kan BVN dai dai ne da wanda yake kan account, kada a samu date of birth dinka dake kan BVN 21 - May - 1998 misali, date of birth dinka dake kan account kuma 21 - May - 1990.
Wannan ma akwai matsala, dole ya zam na kan BVN dana account daya ne.
.
3. Idan kana da account biyu ko uku a bankuna daban daban, misali kana da account da Islamic Bank Ja'iz bank, kana da GT, kuma kana da UBA, toh kafin ka cika N-POWER sai ka tsaya ka duba wanne account ne yake dauke da information din da yake dai dai dana kan BVN dinka, sai ka cika N-POWER dashi.
.
4. Abu na hudu, kada kayi kuskure wurin saka phone number dinka, yayin cika N-POWER, ka saka lambar da koda yaushe kana aiki dashi, wanda zaka iya yin welcome back dinsa Koda ya bata ko ya lalace, sannan kada yi mistake yayin saka email dinka, kamar yadda aka sani ba'a rubuta email da Capital letters, so, a lura.
Kafin kaje cika N-POWER ka tabbatar email dinka yana aiki, bai mutu ba, saboda kasan idan kayi watanni uku baka hau email dinka ba toh ya lalace sai ka sake sabo.
Haka kuma kada kayi kuskure wurin shigar da BNV dinka.
Idan aka samu kuskure a wani abu da sauki, amma idan aka samu kuskure a BVN shike nan mutum zai iya rasawa.
A lura sosai.
.
5. Abu na kusa da karshe, shine, galibi mutane suna rudewa wurin suna (Surname) da (Other name) da (Middle name) ko (First name).
Hanya mafi sauki ka dauki National ID Card dinka ka rika saka abinda ka gani akai.
Idan akan ID Card dinka an rubuta (Surname : Abdulhadi) toh haka zaka saka bayan ka auna shi da information dinka na banki, idan (First  name Isah Ibrahim ne) to hakan zaka yi.
.
6. Abu na karshe shine, galibi za'a samu cunkoson mutane a wuraren masu computer, a ranar, da sauran ranekun, toh ka tabbatar idon yana kallon abinda ake shigar maka, domin ta yiwu mai computer kansa yayi zafi, ko ya gaji, ko yana sauri ace ya gama ya karbi kudi, toh kasa ido idan ya saka kuskure ka gaya masa.
Sannan idan an kammala shigarwa, kada a dannan submit, har sai an koma daga farko, an duba kowanne, an tabbatar dai dai ne, sai a dannan submit.
.
6. Kada a dogara da wadannan zalla, aje ayi ta addu'a, da fatan Allah yasa a dace, sallar dare, sadaka, zikirori, domin yawan wadanda zasu nema sun ninka wanda ake so a dauka sau 20 koma sama da haka.
Idan Allah ya zabe ka shike nan, ban wanda zai hana ka.
Akwai rubutun da zanyi akan yadda za'a cika bisa ga abinda kake dashi na certificate da kuma wane wuri ya kamata ka cika.
Copied

Post a Comment

1 Comments

Emoji
(y)
:)
:(
hihi
:-)
:D
=D
:-d
;(
;-(
@-)
:P
:o
:>)
(o)
:p
(p)
:-s
(m)
8-)
:-t
:-b
b-(
:-#
=p~
x-)
(k)