Yadda zaka nemi aikin NPOWER 2020

Yan uwa barka da warhaka batareda bata lokaci ba yadda zaka nemi aikin NPOWER 2020. Zasu fara daukan sabbin diba wanda za fara ranar 26/06/2020 da misalin karfe 11:45 na yamma kuma koda koda bakayi makarantaba zaka iya cikawa domin cikawa shiga nan Apply here idan kashiga zaka fara bude profile abun da ake bukata wurin bude profile shine Email wanda dole ne wannan kuma kasamu email mai amfani saboda za aturoma  verification link ta Email din sauran karin bayini yana kan wannan photon
Domin kuma a cikama akan farashi mai sauki sauka tuntubi wannan number kiraa ko WhatsApp 07045527535 
Ga bayin photon a rubuce kuma cikin harshen hausa

Za'a bude wannan shafi na rijistar shirin N-power (http://www.npower.fmhds.gov.ng) da misalin karfe 11:45pm na daren ranar 26 June 2020

Sun bayyana cewa rijistar N-power kyauta ne,zaka iya yi da kan ka ko kuma ka bawa 'yan kasuwa suyi maka

MAI SHIRIN RIJISTAR N-POWER WAJIBI NE YA KULA DA WADANNAN ABUBUWA:

1 Kar shekarun haihuwarka su wuce 18 zuwa 35 ma'ana ya zamo ace a tsakankanin shekarun 1985 zuwa 2002 aka haifi mai yin rijistar

2 Wajibi ne ka tanadi wadannan abubuwan kafin fara rijistar N-power

(A) Kwafin cikakkun bayanan lambar nan ta bai daya wato BVN tana da matukar muhimmanci 

(B) Hoto Wanda bai wuce nauyin MB1 ba

(C) Adireshin Email na kirki ko kuma lambar wayar da ake amfani da ita

(D) Takardun shaidar Kammala karatun Digiri da kuma na yiwa kasa hidima ga masu bukatar cike tsarin N-power na (N-Teach da kuma N-Health)

3 Da zarar lokacin bude shafin rijistar yayi to za'a dannan wannan hanya don fara rijistar:  

http://www.npower.fmhds.gov.ng

4 Da zarar Adireshin ya bude maka anan ne zaka ci karo da ka'idoji da kuma dokokin aikin N-power sai ka danna cewa ka amintu da wadannan dokoki

(A) Zaka shigar da Adireshinka na Email ko kuma lambarka salula ta gaskiya wacce za'a same ka a kanta

(B) Wadannan bayanai zasu yi maka nuni da ka koma ka bude wancan Adireshin naka na Email don tabbatar da cewa kai din ne

(C) Da zarar ka tabbatar musu da cewa kai din ne a Adireshin naka na Email  sannan za'a bukaci ka shigar da lambobin nan naka guda 11 na lambar bai daya ta BVN sai kuma ranar haihuwa wacce zaka fara shigar da rana-wata-shekara (dd/mm/yy 

Sai dai ka lura da wani abu, idan lambar nan taka ta BVN ba daidai bace to ba zaka sami damar cigaba da wannan rijista ba

(D) Zaka shigar da Sunan Babanka sannan sunanka sai kuma Sunan Kakanka idan kana amfani da suna uku kenan (Surname, first name, middle name) dukkanin su lallai ne su zamo daidai da bayanan ka na lambar bai daya ta BVN

(E) Za'a bukaci ka nuna alamar cewa kayi karatun zamani ko kuma baka yi karatun zamani ba, sai dai ka sani cewa N-power ta kowa da kowa ce

(A) Masu karatu ne kadai zasu cike N-power fannin karantarwa da kuma Lafiya (N-Teach da N-Health) kadai

Wanda zai cike N-power bangaren lafiya lallai ne ya mallaki shaidar karatu ta Digiri, OND, HND a bangaren Misali 

Medicine
Microbiology
Nursing
Public Health
Botany
Midwife
Psychology da sauran bangarorin lafiya

Za'a bukaci ka dora shaidun karatun naka lokacin da hali ya bayar da bukatar hakan

(F) Za'a bukaci ka amsa wasu tambayoyi tare da dora hoton katin shaida

 Sai dai kowa ya sani cewa katin shaidar da aka yarda da su a Gwamnatance sune:

International passport
National ID Card
Valid Driver's license
Parmanent voters card

(G) Ka tabbatar ka bibiyi bayanan da ka shigar kafin ka tura

Da zarar ka tura bayanan naka to zasu turo maka da wata lamba wacce ake son ka rubuta ta ka adana

A kula da kyau wannan shekarar tsarin ya canja akan na baya, kuskure kadan aka yi za'a iya rasa wannan aiki na N-power

A kula da kyau a kuma yi addu'a, Allahu ya bada nasara ya kuma karawa rayuwa albarka
Copied

Post a Comment

0 Comments