EFCC Ta Kame Surukin Atiku Abubakar

Hukumar yaki da masu yiwa arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta damke Alhaji Babalele Abdullahi surukin dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party, Atiku Abubakar a yau Asabar.
Babalele dai shine diractan kudi na Atiku Group of Companies.
Daily Trust ta ruwaito cewa an kama Babalele ne a gidansa da ke Maitama a babban birnin tarayya Abuja.
An gano cewa jami'an EFCC da adadin su ya kai 24 ne suka isa gidan Babalele a cikin motocci biyu; Toyota mai lamba CS 522 RSH da kuma Hilux guda daya.
Sun isa gidan Babalele da ke Maitama ne misalin karfe 8.30 na safiya amma ba a bari sun shiga ba har sai da lauyoyinsa suka iso.
"Sun taho da izinin bincike gida da ofishin Babalele amma ba su samu wani abu na laifi ba.
Daga nan kuma sai suka wuce ofishinsa dake Oakland Centre a Maitama nan ma ba su samu wani abu na laifi ba. Sai dai sun karbe takardun filayensa.
Bayan haka, sun kuma sake zuwa gidansa da ke Wuse inda nan ma suka gudanar da bincike amma ba su samu wani abin laifi ba.
Bayan haka ne zai jami'an na EFCC suka tafi da Babalele zuwa ofishinsu da ke Wuse domin ya basu wasu bayyanai a rubuce tare da Mr Lawan Ayuba," kamar yadda kakakin Atiku Paul Ibe ya sanar.
Wani babban jami'in EFCC da ke tuntuba ya ki cewa komai a kan kamen. Kakakin na EFCC kuma bai amsa wayarsa ba ko sakon kar ta kwana da aka aike masa a yau Asabar.

Post a Comment

0 Comments