PDP TACI ZABEN GWANMA A JIHAR ADAMAWA

Babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya PDP ta yi nasarar kwace kujerar gwamnan jihar Adamawa bayan kammala zaben cike gibin da aka gudanar a ranar 28 ga watan Maris, 2019.
Dan takarar kujerar gwamnan a jam'iyyar ta PDP, Amadu Umaru Fintiri ya samu nasarar ne da kuri'u dubu 376,552, yayin da gwamna mai ci, Umar Jibrilla Bindow na jam'iyyar APC mai mulkin jihar a yanzu ya zo na biyu da kuri'u 336,386.
Jam'iyyar ADC ce ta zo ta uku a zaben inda dan takararta Abdul'aziz Murtala Nyako ya samu kuri'u 113,237.
Bayan karanta dukkan sakamakon da aka tattara na 'yan takarar da suka tsaya neman kujerar jihar ta Adamawa, Kwamishinan Zaben jihar, Farfesa Andrew Haruna, ya bayyana Amadu Umaru Fintiri a matsayin wanda ya samu nasarar zama gwamnan jihar a zaben.
Abin da Buhari ya ce kan zaben Kano da Sokoto da Adamawa

Jihar Adamawa dai na daga cikin jihohin Najeriya shida da suka rage da ba a kammala zaben gwamna ba a Najeriya, inda a ranar 11 ga watan Maris ne Kwamishinan Zaben jihar, Farfesa Andrew Haruna, ya bayyana zaben jihar a matsayin wanda bai kammala ba, sakamakon yawan kuri'un da aka soke kusan 40,000 ya fi tazarar da ke tsakanin 'yan takarar PDP da APC yawa.
Kazalika kafin ranar da hukumar zaben, INEC ta ware domin gudanar da zaben cike gibin da aka yi a ranar 23 ga watan Maris, babbar kotun jihar Adamawa ta bayar da umarnin dakatar da gudanar da karashen zaben gwamnan a jihar saboda karar da dan takarar gwamna na Jam'iyyar MRDD a jihar ya shigar inda ya bukaci kotu ta soke zaben da aka yi saboda rashin sanya alamar jam'iyyarsa a takardar zaben.
To sai dai kuma a ranar 26 ga watan Maris ne kuma, wata kotu a jihar ta Adamawa ta sauya matsayarta bisa umarnin da ta bayar na dakatar da kammala zaben gwamna a jihar , inda ta bayar da damar kammala zaben.
Da wannan nasara jam'iyyar PDP dai ta yi nasarar kawar da gwamna mai ci Umar Jibrilla Bindow na jam'iyyar APC mai mulkin kasar.

Post a Comment

0 Comments