Yanzu Waye Dan Takarar PDP A Kano Bayan Kotu Ta Kori Abba K. Yusuf ?

Kotu Ta Kori Abba K. Yusuf Daga Takarar Gwamnan Kano
Babbar Kotun Tarayya dake Kano ta kori Abba Kabir Yusuf a matsayin Dan Takarar Gwamnan Jihar Kano a Jam’iyar PDP sakamakon kura kurai da kotun ta gamsu da su lokacin da aka yi zaben fidda Gwani na Jam’iyar a Kano yayin da ya rage saura kwanaki biyar a gudanar da zaben gwamnan. Inda Kuma nan take ta ayyana Ibrahim Al'Amin Little a matsayin halatatcen dan takarar gwamna PDP a jihar Kano.
A ranar Asabar me zuwa ne dai za'a gabatar da zaben gwamna a jihar ta Kano, har kawo wannan lokaci bamu iya samun jin ta bakin tsagin da Abban ya fito ba wato Kwankwasiyya musammman ma jagoran nasu Engr Dr Rabi'u Musa Kwankwanso. Abba Kabir Yusif shine wanda jagoran jam'iyyar PDP a Kano Rabi'u Kwankwanso ya zaba a wani zaben fidda gwani da suka shirya, wanda bai yiwa da yawa daga 'yan jam'iyyar PDP dadi ba wanda hakan ya fusata wasu suka tafi kotu bisa zargin rashin Adalchi yayin zaben, wasu kuma suka bar jam'iyar gaba đaya.

Post a Comment

0 Comments