Yadda zaka gane Fake alert wato Alert ɗin bogi

 Yadda zaka gane Fake Alert wato Alert na bogi Mafi yawancin mutane suna ƙorafi akan alert na bogi musammam ƴan kasuwa kuma a wannan yanayi da muka shiga sabo na cashless wanda yanzu anfi amfani transfer da POS saboda rashin tsabar kuddi a hannu, don haka ga wasu hanyoyi da zaga gane kohma ka kare kanka daga Fake alert

Na Farko 

Lura da kyau karkayi sauri wurin ganinnka sallami wanda yama transfer ba tareda ka tabbatarda sahihancin transfer saba don haka kanaga ganin Alert saika fara dubah sunan da akaturo saƙon dashin shin sunan bankin kane idan sunan bankin kane ba spelling errors koh an raba kaman haka FIR.ST Bank koh FIRS_T kodai maka mancin haka saika tafinkan Balance kaga shin balance ɗinka ya ƙaru ma ana idan kanada 5000 kuma amfa transfer 20000 saika dubah kaga shin kuɗin ya koma 25,000, sannan wani sa in ana iyayin cinikin akan zai turama dubu goma koh dubah ɗari saiya turama 1000 a madadin 10000 saboda kai a lokacin baka lurabah toh abunda yakamata anan dole ka maida hankali kuma ka samu littafi kana rubuta kuɗin dashiga account ɗinka da wanda ya fita da kuma balance ɗin dayake ciki idan mutum zaima transfer saika duba kaga nawane wanze a account ɗinka sannan nawa zaima transfer misali acikin account ɗinka akwai 10k zaima transfer 20k toh kaga yakamata balance ɗin account ɗinka yazama 30k ne kada ka kuskura batareda kaga wannan balance ɗin bah kabada kaya 

Sai abu na gama kuma shine dubah balance ta hanyar USSD ga masu karamar waya domin tabbatarda shigowan kuɗi dukda hakan zaisa ana jama naira 10 kuɗin dubah balance Na biyu 

Amfani da Mobile App na Banki:- a irin wannan lokaci mobile app bakaramin taka rawar gani yakebah wurin daƙile fake alert da kuma sauƙaƙawa customer wurin jiran saiyaga alert, domin idan kana aiki da mobile app ana turama kuɗi zakashiga ciki ka dubah kuma zakagani indai ya shigo batareda ɓata lokaci bah saɓanin na karamar waya saika jira SMS 

Yadda zaka samu mobile app shine yawancin bankuna sunada nasu app ɗin kuma akwai a playstore da kuma app store saika tabbatarda wanne bankin ka suke amfani dashi saika ɗakko kayi register koh kuma kaje bankin naka kai tsaye domin a saitamashi domin shima wasu scammers na iyayin Application da kuma website ba banki na bogi domin cutan alumma 

Na uku 

Samun POS mashine koda na Moniepoint ne domin basuda matsala sosai kuma kuɗinsa innaga bai wuce 20k bah saika saya idan mutum yazo kacire kuɗinka a ciki indai karamin kudinne yafi sauki akan transfer

Sai kuma abu na karshe shine addu ah domin kuwa duk abunda muka lissafa a baya tabbas wani zai iya tsallakesu dukka yazo a cuceka saboda haka a kula da addu ah tundaga kan na fita daga Gida azkr ɗin safiya da maraice da kuma ta shiga kasuwa sannan koyaushe kazama very intelligent kana lura da abun buwan da suke faruwa da kuma yanayin mutum 

Matakan kariya 

Kada ka kuskura kabawa customer ka ma anwanda zaima transfer lambar layin da kake amfani dashi a banki domin ta hakan zai iya turama wannan fake alert ɗin, sannan kada ka kuskura kana bari abokin kasuwanci wato customer yana ganin cikin wayanka domin hakan zai iyasa yaga wani abu dazai iya taimakamai wurin yin wannan ɓarna 

Allah ya karemu da kariyarsa 

A.I.H

Idan kanada tambaya ka ajiye a wurin comments section koh kuyi join Telegram channel namu domin karin bayani koh tambaya.

Post a Comment

0 Comments