Yadda zaka samu certificates a Digital Nigeria

 Ministan Sadarwa Sheikh Pantami Ya Kaddamar Da Sabuwar Manhajar Yanar Gizo Ta Wayar Salula Domin Koyawa Al'ummar Najeriya Sana'o'in Zamani

Ministan Sadarwa Sheikh Isa Ali Pantami ya kaddamar da sabuwar manhajar yanar gizo da ta wayar salula ga 'yan Nigeria domin koya musu sana'o'in zamani, wanda aka yiwa take da "Digital Nigeria Portal And Mobile App".

Wannan tsarine da 'yan Nigeria zasu koyi sana'o'i daban daban na zamani da samun ayyukan yi cikin sauki, kuma an tsarashi yadda kowa zai iya koya da kanshi ta hanyar gani a bidiyo da rubutu, tsarin yana da matukar muhimmanci ga 'yan Nijeriya, duk wanda ya kamalla training a kowanne tsari za'a bashi Certificate.

Akwai tsaruka guda ukku da suka hada da

1, Digital Nigeria

2, NITDA Academy

3, IBM Digital For Africa

A karkashin tsarin DIGITAL NIGERIA, akwai tsaruka masu yawa, tun daga yadda tsaka koyi yadda zaka dinga aiki da Computer, yadda zaka samu bayanai ta yanar gizo, yadda zaka bayar da kuma yada bayanai ta yanar gizo, yadda zaka kiyaye kanka daga sharrin 'yan damfara a yanar gizo, yadda zaka kirkiri wani abu ko manhaja, da Computer da dai sauran manya manyan ayyukan da suka shafi computer.

Tsarin NITDA ACADEMY, yana da tsaruka guda ukku da suka hada da;

1, SDAs Training

2, Students Training

3, Generall Training



Haka shima tsarin IBM DIGITAL FOR AFRICA, tsarine wanda Kamfanin Amurka ke koyarwa domin fahimtar manhajar zamani a afrika.

Kowanne tsari yana da matukar muhimmanci, kuma za'a bawa duk wanda ya kammala Certificate bayan kammala training din.

Ga duk wanda yake bukatan shiga tsarin ya shiga cikin wannan adireshin na yanar gizon ayi regista

Shiganan

Copied RARIYA cmrd Abba pantami

Post a Comment

0 Comments