Yadda zaka cika tallafin NG-CARE na kasuwancinka cikin sauki batareda kasha wata wahalabah
Da farkodai mutaneh da yawa suna korafi akan cewa wasu da yawa wurin cikawa suce yaku submitting ko dai wata matsala ta daban toh insha Allah ga bayani dalla dalla akan yadda zaka cika
Da farko ka shiga https://www.ngcaresbusiness.org/ idan kashiga zai nunamah wuri kaman yadda zaku gani a photon dake kasa
Na biyu
Shi wannan link din baya bukatan dogon zance nako wanne state yana wurin kawai ka taba kan select state yana budewa saika zabi state ka da kake kasuwanci a ciki bawai jahar da aka haifekabah a a wanda kake kasuwanci a ciki shi zaka zaba kamar yadda zaku gani photon dake kasa
Anan zaka zabi dukkan state naka kana ganin state din saika taba kanta
Na uku
Zai kaika wurin da zaka zabi halin da kasuwanci ka yake ciki wato wani matsayi yake ciki da kake bukatan tallafi
Na farko idan kaci bashi a harkan kasuwanci ka bayan 15 june 2020 kuma kana bukatan tallafin kudi, abunda ake nufi anan shine bashin da kaci ya kasance daga 15 june, 2020 zuwa yanzu
Saina biyu kuma bakaci bashin kowabah kuma kana biyan ma aikatanka sannan kana biyan wasu bukatu na kasuwancinka amma kuma kana bukatan tallafin kudi domin habaka wannan kasuwanci
Sannan ba kowanne state bane takeda irin wa yannan abu biyun zasu nasu da banbanci sai a kula kazabi wanda ya dace da kasuwancinka
Dan haka saika zabi wanda kake ciki saika taba kan Apply dinnan
Abu na hudu
Shine yadda zaka bada yana nan ka da ake bukata
Kamar yadda zaku gani a photon dake sama sune abubuwan da ake bukatan ka cike kuma duk wanda kaga star ja a kansa tohfa wannan bayanin dolene saika cike shi kuma wannan form idan ka kike wani abu ba yadda aka tsarasabah bazai baka daman submitting ba sai a kiyaye
Ga bayanin ko wanne daya daga cikin wadan abubuwa
* Business name: sunan kasuwancin da kake
* What kind of business: wani irin kasuwanci kake su wayannan ba rubutawa zakayi bah zaka zabane acikin wanda suka rubuta a wurin
* What kind of.... :- shi wannan saika zabi zasuwancinka sannan zai baka dama misali ka zabi TRADING tozai fitone da WHAT KIND OF TRADING saika zaba misali building materials
* How much sale in (naira) do you currently make a month:- wato nawa kake samu a wata a yanzu ta hankar kasuwancinka misali kanasamun 200,000 a wata saikasa
* What date/year you currently open your business: shekaran da ka bude business dinka zakasa
* Phone number of head of the business: number wayar shugaban kasuwancin ma ana oga
* Number of employees: adadin ma aikatan da kakedasu a wannan kasuwanci naka
* First name of head of the business: sunan farko na shugaban kasuwancin a lura anan first name kawai akace sunan ka kawai zakasa a wurin
* Last name of head of the business sai sunan karshe na shugaban kasuwancin wata sunan baba
* Email of head of the business: email na shugaban kasuwancin anan kalura wurin sakah wannan email din misali arewatech360@gmail.com
* Date of birth of head of the business: shekarun haihuwa na shugaban kasuwancin, idan ka taba kan year saika taba kan month sannan day inbakataba dukkah bah bazayyibah
* Gender of head of the business: jinsin shugaban kasuwanci ma ana mace ne koh namiji
* State of the business: jahar da ake kasuwanci
* Local government of the business: karamar hukumar da ake kasuwanci
Daga nan idan ka cika komai daidai zakaga madannin submit button din yayi kore saika taba submitted kayi submit nashi
Allah ya bada sa a
©️ A.I.H
Idan kanada tambaya ka ajiye a wurin comment ko kuyi joinTelegram channel namu domin karin bayani koh tambaya.
0 Comments