Yadda zaka samu TIN number kyauta

 Yadda zakayi registration na TIN number ka samu kyauta da kanka batareda ka biya kudi bah Mutane da yawa wasu ba susan ya ake samun TIN number ba ba wasu kuma ma basu san me TIN number bah kawai sai insunzo cika wani abu ace ana bukatan wannan TIN number kuma basu dashi 

Da farko menene TIN number 

Tax Identification Number (TIN) wata number ne da ake iya kane mutum da ita koh kamfani kaman dai NIN number kowa da nasa domin biyan kudin Haraji a Nigeria 

Menene amfanin TIN number 

Wato ita TIN number amfaninta yanada yawa wanda suke kasuwanci koko ince masu company susan hakan sosai  

1. Akwai biyan haraji ita daman wannan number da za a baka anke bance ma ita ne domin biyan haraji akan abubuwa maban banta koko ince akan kasuwancin na kamfaninka 

2. Samun daman cike wani tallafi na gwamnati, sau tari zaka idan kazo cike wani tallafi na kusuwanci koma na daidaiku sai ace kasa TIN number naka a wurin soboda agane shin kana biyan haraji koh baka biya 

3. Bude Account na kamfani ko maka mancinsa, akwai account dinda idan kaje budema shi dai ana bukatan wannan TIN number din kafun ka samu daman bude wannan account din. 

Dadai sauransu 

Ya ake registration na TIN number 

Yadda ake registration na TIN number ya kasu kashi biyu 

1. individual

2. Non individual 

Yadda ake registration na individual shine da farko zaka shiga wannan link din https://tin.jtb.gov.ng/ zai budema cikin shafinnasu saika duba zakaga inda aka rubuta individual a ciki kamar yadda zaku gani a photon dake kasa 


Kana taba kansa zai kaika wurin da zakasa sunan ka da BVN dink da kuma date of birth naka saika taba kan search. Dolene sunan ka zakasa ya ma daidai da sunan dake jikin bvn dinka 


Kana taba kan search idan abubuwan da kasa daidaibe a take zakaga madannin NEXT ya fito a daidai gefen search dinnan saika dannan kan NEXT din atake zai budema inda zaka cike form din zakaga sunan ka da ka cike a jikin BVN dinka sannan zaka daura photon ka da sauran bayanai 


Kama gama cike sauran kawai saika submit dinsa shikenan 

Gargaɗi: a tabbatarda ansa number waya da kuma email mai amfani a yayin cikewa 

2. Sai kuma na biyu wato Non individual 

Yadda ake registration na Non individual shine 

Da farko zaka shiga wannan link din https://tin.jtb.gov.ng/ shima kamardai na farkon shi wannan dama na kamfanunuwa ne da dai sauransu 

Toh saika shiga inda aka rubuta register for Non individual kamar yadda zaku gani a photon dake kasa 


Kana danna wa shi bai kutan kayi wani verification kaman na farkon kawai zaikaika shafinne kai tsaye inda zaka cike wannan form din 


Saika sa bayan kamfaninka da registration number sa da komai da ake bukatan cikewa sannan kayi submit dinsa 

Gargaɗi:- a lura da kyau yayin sa bayanai kada a samu kuskure sannan a tabbatarda cewa ansa bayanai masu inganci. 

Allah ya bada sa a 

✍️✍️✍️©️ A.I.H 

Idan kana tambaya ka ajiye a wurin comments section koh kuyi joinTelegram channel namu domin karin bayani koh tambaya.

Post a Comment

0 Comments