Nigerian Immigration service zasu fara diban sabbin ma aikata

 Nigerian Immigration service (NIS) zasu fara diban sabbin ma aikata a wannan shekaran 


Related Yadda zaka nemi aiki a company Ɗangote group 

Yadda zaka haɗa CV curriculum vitae a wayanka cikin sauki

Hukumar CDCFIB wanda ta haɗa da civil defence immigration correctional da fire service, wanda suka buɗe portal din civil defence kwanaki toh yanzuma zasu buɗe portal na immigration service, zasu buɗe portal din ne ranar monday 16 ga watan ɗaya January 2023 in Allah ya yarda. 

Soda haka ake cira da duk mai sha awar wannan aiki kuma ya cike ƙa idogin da ake buƙata da su nemi wannan aiki tahanyar shiga portal din su domin apply

Ga matakan aiki da akedasu (position) 

Category A: SUPERINTENDENT CADRE 

I. SI conpass shine wanda suke da kwarewa akan fannin lafia wato doctors kuma sun gama NYSC ɗinsu wanda suka karanci MBBS kenan

II. DSI conpass: shikuma wannan wanda suka karinci sanin magun guna wato pharmacist kuma suka gama NYSC ɗinsu

III. ASI conpass o8 shikuma shine wanda duk wani mai degree koh HND wasu fanni daban kaman computer science, physics, history da sauransu zasu cika 

Category B INSPECTOR CADRE 

Sukuma wanna sune na masu NCE da kuma diploma koh Advance NABTEB 

Category C ASSISTANT CADRE

I. Immigration Assistant iii compass shikuma idan kanada GCE koh NECO da sauransu wato wanda suka gama secondary school kuma sukeda credit guda huɗu 4 kada ya wuce zama biyu 

II. Immigration Assistant iii conpass o3 shikuma wannan shine na masu trade certificate a driving koh mechanic kuma suma ya kasance sun gama secondary school wato SSCE 

Yadda zaka nemi aikin Immigration service

Da farko zaka shiga wannan link din https://cdcfib.career domin cikewa saidai kamar yadda muka faɗa a baya sai ran Monday za abuɗe portal din kuma za arufene bayan sati biyu da buɗewa wato karshen wata kenan zai kama insha Allah

Abubuwan da ake buƙata yayin cikewa

1. Dole ya kasance kaiɗan Nigeria ne 

2. Kanada National I'D card 

3. Yakasance kanada takardan makarantanka a hannu na abunda kakeso ka nema 

4. Dole ya kasance kanada certificate daga asibiti na medical fitness kuma asibitin ya kasance na Gwamnati 

5. Dole ya kasance kanada ɗabiu mai kyau kuma ba a taba kamaka da wani babban laifi bah 

6. Dole ka haye gwajin kwayoyi wato dai sai anma gwaji saboda a tabbatarda baka shaye shaye 

7. Ba aso yazama kanada nakasu a wurin al amrar kuɗi 

8. Ya kasance ɗan shekara 18 zuwa 30 koh kuma 35 ga likitoci da masu magun guna (doctors and pharmacist) kuma kada tsawo yayi kasada 1.65m ga maza 1.60m kuma ga mata 

9. Faɗin ƙirji kada yayi kasa da 0.87 ga maza 

10. Sannan anaso. Yakasance kanada illimin computer kaɗan wannan ba dole bane inkanadashi zaka samu wani amfanin da wanda basudashi barasu samubah 

11. Ka tabbatarda cewa duk wani certificate da kake dashi ka gabatardashi alokacin da ake dubah takardunka domin baza a karɓa bah idan har angama 

Sannan za ayi jarabawa a computer wato computer based test CBT ga wanda sunayensu ya fito 

Sannan wannan application ɗin kyautane ba a biyan kuɗi koh sisi yayin cokewa saidai idan kaje shagon computer za acikewa ka biyasu kuɗin cikewa bawai kuɗin za hukumar ake biyaba 

Allah ya bada sa a

✍️✍️✍️©️ A.I.H 

Idan kanada tambaya ka ajiye a wurin comments section koh kuyi join Telegram channel namu domin karin bayani koh tambaya. 

Post a Comment

0 Comments