Yadda zaka cika sabon tallafi daga MTN foundation

 Yadda zaka cika sabon tallafin daga MTN foundation, Meta da Microsoft 

MTN Nigeria


Kamfanin MTN Nigeria ta hannun MTN foundation zai bada tallafi na training dakuma kayan aiki koh kuɗi ga matasa a wasu daga cikin kasannan a wasu daga cikin jahohin Nigeria

Shirin na ICT and Business Skills Training phase 6 haɗin gwiwa ne tsakanin kamfanoni kamar su 

Microsoft 

Meta (Facebook) 

MTN foundation 

Wannan training za ayi shine tsawon wata biyar kuma a online za ayi shi sannan kamfanin MTN zatana tura muku data har kugama wannan training ɗin da aka shirya wanna mutun dubu uku zasuyi sannan acikin mutun dubu uku za a zaɓi mutun ɗari uku da sukafi kokari araba musu kayan aiki na kimanin million 90 

Kenan kowa zai samu kayan aiki na kimanin dubu ɗari uku 300k kenan amma faa wanda sukafi koƙari mutun ɗari uku 300 sune kaɗai zasu samu wannan daman 

Sharuɗan cika wannan shiri wato abunda ake da bukata sune

1. Matashi daga shekara 18-35  

2. Yakasance kanada kasuwancin da kakeyi wadda ya kasance yana aiki kar yayi kasa da shekara biyu 

3. Yakasance kasuwancinka yana ɗaya daga cikin wannan jahohi 

Yobe 

Niger 

Kebbi 

Ebonyi 

Edo 

Ekiti

Yadda zaka cike wannan shiri na ICT and Business Skills Training phase 6 shine 

Da farko kabi link ɗinnan ka shiga https://www.mtn.ng/mtnf-ict/ kana taɓawa zai kaika shafin MTN foundation saika kasa inka gama karanta zakaga inda aka rubuta click here to apply saika danna 


Kana danna zai kaika inda zaka fara cike wannan form ɗin saika fara cikewa amma ka tabbatarda kasa bayanai masu inganci da kuma email address mai amfani

Kana gama cikewa ka taɓa kan Next step zai kaika inda zakasa address naka dana kasuwancinka 

Shima kana gamawa ka taɓa kan Next zuwa mataki na gaba kenan 

Mataki nagaba bayanai akan kasuwancin ka da kake saika cike shi shima kasa bayanai na gaskiya a wurin 

Sai matakinna kusa dana ƙarshe shine abunda yasa kakeson yin wannan training ɗin saika zaɓa abunda yasa sannan ka danna kai Next 

Mataki na ƙarshe shine matakin karatu wanda zaka zaɓi matakin karatunka misali SSCE koh Degree dabsauransu 
Daganan saika taɓa kan Accept our terms and condition sai kai submit shikenan ka gama saika jira mataki na gaba za za a tuntuɓeka ta email koh lambar waya da kasa 

Allah ya bada sa a

A I.H 

Idan kanada tambaya ka ajiye a wurin comments section koh kuyi join Telegram channel namu domin karin bayani koh tambaya.

Post a Comment

0 Comments