Yadda zaka cika aikin Nigerian Immigration service NIS

 Yadda zaka cike aikin Nigerian Immigration service NIS wanda CDCFIB civil defence immigration correctional da fire service suka buɗe

Kamar yadda mukace muku insha Allah idan an buɗe portal zamu kawo muku yadda zaku cika toh insha Allah ga bayani kamar haka

Related: Nigerian Immigration service NIS zasu fara diban sabbin ma aikata

Nigerian Immigration service NIS recruitment application for 2022/2023

Ga karin bayani gameda matakan daukan aikin da kuma abunda ƙa idojin da akeso ka cikesu 

Ga matakan aiki da akedasu (position) 

Category A: SUPERINTENDENT CADRE 

I. SI conpass shine wanda suke da kwarewa akan fannin lafia wato doctors kuma sun gama NYSC ɗinsu wanda suka karanci MBBS kenan

II. DSI conpass: shikuma wannan wanda suka karinci sanin magun guna wato pharmacist kuma suka gama NYSC ɗinsu

III. ASI conpass o8 shikuma shine wanda duk wani mai degree koh HND wasu fanni daban kaman computer science, physics, history da sauransu zasu cika 

Category B INSPECTOR CADRE 

Sukuma wanna sune na masu NCE da kuma diploma koh Advance NABTEB 

Category C ASSISTANT CADRE

I. Immigration Assistant iii compass shikuma idan kanada GCE koh NECO da sauransu wato wanda suka gama secondary school kuma sukeda credit guda huɗu 4 kada ya wuce zama biyu 

II. Immigration Assistant iii conpass o3 shikuma wannan shine na masu trade certificate a driving koh mechanic kuma suma ya kasance sun gama secondary school wato SSCE 

Abubuwan da ake buƙata yayin cikewa

1. Dole ya kasance kaiɗan Nigeria ne 

2. Kanada National I'D card 

3. Yakasance kanada takardan makarantanka a hannu na abunda kakeso ka nema 

4. Dole ya kasance kanada certificate daga asibiti na medical fitness kuma asibitin ya kasance na Gwamnati 

5. Dole ya kasance kanada ɗabiu mai kyau kuma ba a taba kamaka da wani babban laifi bah 

6. Dole ka haye gwajin kwayoyi wato dai sai anma gwaji saboda a tabbatarda baka shaye shaye 

7. Ba aso yazama kanada nakasu a wurin al amrar kuɗi 

8. Ya kasance ɗan shekara 18 zuwa 30 koh kuma 35 ga likitoci da masu magun guna (doctors and pharmacist) kuma kada tsawo yayi kasada 1.65m ga maza 1.60m kuma ga mata 

9. Faɗin ƙirji kada yayi kasa da 0.87 ga maza 

10. Sannan anaso. Yakasance kanada illimin computer kaɗan wannan ba dole bane inkanadashi zaka samu wani amfanin da wanda basudashi barasu samubah 

11. Ka tabbatarda cewa duk wani certificate da kake dashi ka gabatardashi alokacin da ake dubah takardunka domin baza a karɓa bah idan har angama 

Yadda zaka cika aikin Nigerian Immigration service NIS 

Da farko kashi portal na CDCFIB civil defence immigration correctional da fire service dasu sune sukeda alhakin ɗaukan ma aikata na dukka wannan fanni. ka shiga link din nan https://cdcfib.career/ kana shiga zai kaika shafin nasu da zaka gani kamar haka 


Toh saika taba kan Apply Now inda zaikaika shafin kamar haka, sannan kamaida browser desktop site idan a waya kakeyi yadda zaka maida browser naka desktop site shine ka dubah saman chrome browser dinka zakaga wasu ɗigo ƙwaya uku ta gefen dama saika taba kansu zasu baka wasu options a ciki ka dubah zakaga inda akasa Desktop site saika taɓa shikenan Toh anan kaza buɗe profile ne saika lura da kyau ka cike komai daidai wurin da zaka zaɓi categories kuma yanada kyau ka tsaya ka karanta kowanne categories kafun ka fara zaba sannan zurin password shima dole saikasa password mai ƙarfi kamar haka Arewatech360@ saikayi save and continue shikenan ka buɗe profile ɗinka , daganan zaikaika shafin da zakasa person details dinka wato bayanai akan kanka sannan zai baka application code kamar yadda zaku gani a photon dake kasa


Toh saika ɗau Application code ɗin naka koda network ya baka problem zaka dawo ka cike abunka, kana gamawa saika danna kan save and continue zaikaika wurin sakah passport photo kenan koh ya kaika wurin primary school information saika sa wannan bayaninna makarantanka sunanta da shekarar da ka shiga da kuma wadda ka gama sai certificate shine FSLC wato first school leaving certificate saika danna kan save and continue zaikaika wurin na secondary school information naka kamar haka 


Toh saika shima kamar yadda kasa na primary school ɗinka saika danna kan save and continue zai buƙaci da ka upload na results dinka kamar haka 


Saika dannan inda akasa add NECO results kana dannawa zaikaka shafin da zaka ɗaura results dinka ba dole saika daura dukka 9 bah koh da guda biyar kasa yayi Kamar yadda zaku gani a photon dake kasa


Kana gama ɗaurawa saika taba kan done shikenan ka gama da wannan idan na masu secondary school kake cikewa shikenan saika duba sama inda aka rubuta passport photograph saika taba zai kaika inda zaka upload na photon ka shima kada ya wuce 80kb zaka iya rageshi ta hanyar amafani da photo resizer


Kana gama upload nashi shikenan inkuma kayi tun a farko toh basaika sakeh bah zai nunama shi a summary inka kamar haka


Saika dubah duk abunda kasa daidaine idan daidaine saika submit nashi shikenan ka gama. Saikayi download nashi a PDF kaje ama printing nashi a cafe. 

Allah ya bada sa a

A.I.H 

Idan kanada tambaya ka ajiye a wurin comments section koh kuyi join Telegram channel namu domin karin bayani koh tambaya. 

Post a Comment

0 Comments