Hukumar CDCFIB wanda suka hada da civil defence, immigration, correctional, and fire service sun bude portal domin masu son shiga wannan aikin
An bude shafin ne ranar 14 ga watan july wanda yanzu haka ana cikewa ga masu bukata
Abubuwan da ake bukata domin cikewa shine yakasance kanada NIN da sauran takardunka na makaranta wanda ka gama koh zaka cike dashi, sannan yakasance kai dan Nigeria ne wanda aka haifa anan, karka wuce tsakanin shekara 18 zuwa 35 dole yazama kanada lafiya sannan ba kada wani criminal record
Abubuwan da zakayi scanned ka daura sune
1. Certificate of birth
2. Local government identification (indigene)
3. Passport (hotonka)
Yadda zaka cike wannan abun shine
Da farko kashiga wannan link din https://recruitment.cdcfib.gov.ng/ saika zabi inda aka rubuta new Application
Danan zai kaika inda zaka zabi abunda kakeso ka cike misali
Immigration koh civil defence fire service da sauransu. Saika zaba wanda kakeson cikewa da kuma iya matakin karatunka idan degree ne ka zaba idan Msc ne ka zaba koh secondary, zai baka position din da akedashi a wannan fannin
Kana gama zaba shikenan zai kaika mataki na gaba wato inda zakasa NIN da kuma lambar waya Yana kaika saikasa idan kasa sai ka rubuta abunda yake jikin photon dake kasa daidai inda kaga an rubuta da capital letter ka rubutashi a haka sannan inda kaga ansa small later koh number shika ka tabbatarda ka rubuta saika taba inda aka rubuta validate idan yanuna good shikenan saika dannan kan Next. Idan kuma yaki wucewa yana baka error toh ka chanja phone number din zai wuce in sha Allah
Mataki na gaba shine na saka information na inda zakasa inda kayi Primary misali da shekarun da ka gama da sauransu
Daganan sai kayi review na information dinsa kasa idan komai daidai ne saikayi submit kawai
Allah ya bada sa a
Idan kanada tambaya ka ajiye a wurin comment section koh kuyi join Telegram channel namu.
0 Comments