Hukumar sojan ruwa ta Nigeria wato Nigerian Navy zasu fara ɗiban sabbin ma aikata
Hukumar tana sanarda dukkan masu sha awan shiga wanna aiki cewa zata buɗe portal domin fara registration na Nigerian Navy Basic Training School batch 38 wanda zata buɗe ranar alhami 02 ga wannan October sanna kuma za a rufe in sha Allah ranar 31ga watan Goma wato October 2025 in Allah ya kaimu
Ga wasu daga cikin sharuɗan nema
Dole yakasance kanada 5 credit a SSCE GCE NABTEB koh NECO kuma kada ya wuce zama biyu
Sannan certificate na makaranta kada yayi sama da shekara shida
Dole mai nema yakasance daga shekara 18 zuwa 22 ga masu SSCE saikuma masu NCE diploma Nurse/midwife, sportsmen and women dasu imam Driver mechanic sukuma daga shekara 18 zuwa 26
Yadda zaka nemi aikin sojan ruwa wato Nigerian Navy
Da farko zaka shiga wannan link https://www.joinnigeriannavy.navy.mil.ng/ zai kaika shafinsu kaman haka
Yana kawoka nan akwai duk wasu karin bayani da kakeda bukata domin cike wanann aiki daga nan saika dannan inda aka rubuta Apply now kana tabawa zai kaika inda zaka cike bayanan ka da akeda bukata
saika cike dukkan abunda ake buƙata kai submit idan kuma baka iyaba kaje shagon computer mafi kusa dakai domin su cikema
Wannan neman aikin kyautane bawani kuɗi da ake biya saboda haka akiyaye da macuta da zasuce ka kawo kuɗi koh wani abu makamancin wannan. Saidai indan cafe kaje zaka biyasu kudin aikinsu da sukama da na printing
Allah ya bada sa a
A.I.H
Idan kanada tambaya ka ajiye a wurin comments section koh kuyi join Telegram channel namu domin karin bayani koh tambaya.




0 Comments